Yadda Wata Mata Ta Haihuwa a Filin Buga Kwallon Kafa a Jahar Kano

Yanzun nan muke samun wasu rahotanni daga wasu shafukan Gidajen jaridu na kafafen sadarda zumunta inda rahotannin ke Bayyana Yadda Wata Mata Ta Haihuwa a Filin Buga Kwallon Kafa a Jahar Kano ga yanda Rahoton yakasace
Wata mata ‘yar shekaru 30 mai suna Hadiza Ayuba, ta haifi ‘ya mace a filin kwallo na Dr. Abdullahi Umar Ganduje dake karamar Hukumar Dawakin Kudu lokacin da ake taron raba tallafi wa mata masu juna biyu a yau Asabar.
Taron raba kayan tallafin shi ne karo na hudu da mamba mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa, Hon. Mustapha Bala Dawaki yake shiryawa. “A wannan karo, an shirya tallafawa mata 900 daga mazabu 30 na kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa,” in ji Babannan Bala, ma’ajin jam’Iyar APC na mazabar Dawaki.